Jump to content

Natasha Hastings

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Natasha Hastings
Rayuwa
Haihuwa Brooklyn (mul) Fassara, 23 ga Yuli, 1986 (38 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Mazauni Locust Grove (en) Fassara
Karatu
Makaranta University of South Carolina (en) Fassara
A. Philip Randolph Campus High School (en) Fassara
Sana'a
Sana'a dan tsere mai dogon zango da Dan wasan tsalle-tsalle
Athletics
Sport disciplines 400 metres (en) Fassara
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 
Nauyi 64 kg
Tsayi 173 cm
natashahastings.com

Natasha Monique Hastings (an haife ta ne a ranar 23 ga watan Yulin shekara ta 1986) 'yar asalin kasar Amurka kuma kwararriyar 'yar wasan tsere na mita 400.

Hastings ta fara aikinta tun tana ƙarama kuma ta sami nasara a gasar Olympics ta USATF a tseren mita 400 a rukunin 'yan mata na matasa. [1] Ta halarci makarantar sakandaren ta A. Philip Randolph Campus a Harlem, wanda ke a Garin New York, inda ta sami damar ɗaukar sha'awarta zuwa matakin da ya fi dacewa.[2]

Hastings tana da tashar YouTube, wanda take ya haɗa da hotunan ta a bayan fage na tserenta, motsa jiki, da shiri.[3] Har ila yau, tana da jerin bidiyo da ake kira "Tea Time", lokacin da take magana game da batutuwa daga soyayya zuwa shirye-shiryen tunani, sau da yawa tare da abokai da 'yan wasa kamar Michelle Carter. Ta yi alkawarin aure ga tsohon dan wasan NFL, William Gay, a ranar 22 ga Yuli, 2018, amma ma'auratan ba su taɓa yin aure ba. Suna da ɗa guda tare.

  1. "TrackMom.com". Retrieved 14 June 2010.
  2. "USATF".
  3. "Hastings YouTube Channel". YouTube.